Za a yanke kashi 10 na albashin ma’aikata don bunƙasa ilimi a Yobe

Gwamnatin Jihar Yobe ta ce za ta cire kashi 10 cikin 100 na albashin ma’aikata na watan Nuwamba a matsayin gudunmawarsu wajen gyara harkar ilimi a jihar.

Kwamishinan Harkokin Cikin gida, Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Muhammad Lamin ne ya baiyana hakan a taron manema labarai da ya yi a Damaturu a jiya Litinin.

Lamin ya baiyana cewa gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin a haɗa hannu wajen farfaɗo da harkar ilimi wacce ta lalace sakamakon aiyukan ƴan ta’adda sama da shekara 10 a jihar.

Ya nuna cewa aiyukan ƴan ta’addan da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ya gurgunta rayuwar al’umma, harkokin ilimi da gine-gine a jihar.

A ranar 9 ga watan Nuwamba ne dai Gwamnan Jihar Yobe ɗin Mai Mala Buni ya kafa kwamitin tara tallafin ilimi na mutum 25 da nufin tara kuɗaɗe domin farfaɗo da ilimi a jihar.