Yanzu-Yanzu: Buhari ya ƙaddamar da kuɗin intanet na e-Naira

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da kuɗin intanet na e-Naira da za a riƙa kashewa a yanar gizo.

Buhari ya ƙaddamar da kuɗin ne a fadarsa da ke Abuja a yau Litinin.

Tun da farko Babban Bankin Najeriya CBN ya shirya ƙaddamar da kuɗin a ranar ɗaya ga watan Oktoba, amma ya ɗage bisa wasu dalilai.

Hakan na nufin cewa, kuɗin na e-Naira zai fara aiki daga yanzu.