Yadda za ka tsayar da motar ka idan tayarta ta fashe kana tafiya

Shwarwari shida (6) daga Hausa Daily Times ga masu mota ta yadda za su iya tsar da mitarsu a lokacin da suke tsaka da tafiya kuma malejin gudu da motar take ya zarce 100km/h tayar ta ta fashe.

Shawara ta farko:
Lokacin da taya ta fashe, yi ƙoƙari ka natsu yadda ya kamata kuma ka riƙe sitiyarin motarka gam-gam da hannu biyu.

Na biyu:
Yana da mahimmanci kiyaye ƙafarka daga birki kwata-kwata. Kar ma ka kalli inda birki da totir suke, ballantana ma ka yi tunanin taka ɗaya daga cikin su.

Na uku:
Ka nitsu kuma ka tsaya a kan hannun da kake tafiya ka dai ci gaba da kallon gabanka, kuma hankalin ka ya kasance a jikinka.

Na huɗu:
Idan motar Manual ce, sannu a hankali sai ka canza zuwa ƙaramin Giya amma sai idan ka tabbata motar kai kake sarrafata ba ita take sarrafa kanta ba. Idan kuma motarka Atomatik ce, ka barta a ciki Giya wato (D) kada ka yi tunanin canzawa.

Na Biyar:
Kar ka taka birki, ja da tayar da ta fashe take wa motar zai rage mata gudu.

6. Shawara ta shida:
Lokacin da gudun motar ya dawo zuwa 50 km/h, zaka iya taka birki a hankali har sai lokacin da motar ta tsaya