Wayoyin da za su daina WhatsApp daga watan gobe

Shahararriyar manhajar sada zumuntan nan mallakar mai Kamfanin Facebook, wato Whatsapp ba za ta ƙara yin aiki a wasu wayoyi ba daga ranar 1 ga Nuwamba, 2021, saboda wasu dalilai.

Wayoyin da abin zai shafa sun haɗa da Android da iPhone guda 52 mallakin miliyoyin masu amfani da su a duniya.

Manhajar ba za ta ci gaba da aiki a waɗannan wayoyi ba saboda Kamfanin zai daina bayar da taimako ga masarrafar manhajojin irin waɗannan tsoffin ƙira na wayoyin.

Don samun damar ci gaba da jin daɗin ayyukan manhajar Whatsapp, masu wayoyin da abin ya shafa suna da zaɓi biyu – sabunta masarrafar wayoyin (idan mai yiwuwa ne) ko canza sabuwar waya.

Bisa rahoton da Jaridar “The Sun UK” ta buga, wayoyin da wannan sabon matakin WhatsApp zai shafa sun haɗa da:

1. Galaxy Trend Lite

2. Galaxy Trend II

3. Galaxy SII

4. Galaxy S3 mini

5. Galaxy Xcover 2

6. Galaxy Core

7. Galaxy Ace 2

8. Lucid 2

9. Optimus F7

10. Optimus F5

11. Optimus L3 II Dual

12. Optimus F5

13. Optimus L5

14. Best L5 II

15. Optimus L5 Dual

16. Best L3 II

17. Optimus L7

18. Optimus L7 II Dual

19. Best L7 II

20. Optimus F6, Enact

21. Optimus L4 II Dual

22. Optimus F3

23. Best L4 II

24. Best L2 II

25. Optimus Nitro HD

26. Optimus 4X HD

27. Optimus F3Q

28. ZTE V956

29. Grand X Quad V987

30. Grand Memo

31. Xperia Miro

32. Xperia Neo L

33. Xperia Arc S

34. Alcatel

35. Ascend G740

36. Ascend Mate

37. Ascend D Quad XL

38. Ascend D1 Quad XL

39. Ascend P1 S

40. Ascend D2

41. Archos 53 Platinum

42. HTC Desire 500

43. Caterpillar Cat B15

44. Wiko Cink Five

45. Wiko Darknight

46. Lenovo A820

47. UMi X2

48. Run F1

49. THL W8

50. iPhone SE

51. iPhone 6S

52. iPhone 6S Plus