Wanda ya gina masallacin matafiya na kan titin Kaduna-Zaria ya rasu

Allah ya yi wa mai sanannen masallacin matafiya dake kan titin Kaduna zuwa Zaria, Alhaji Sule Bako, ya rasuwa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito mai hanu da shunin ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja, ranar Laraba, kuma an yi jana’izar sa da misalin karfe 1:00 na rana a Kaduna.

Ya rasu yana da shekaru 84. Ya kuma bar ƴaƴa da jikoki 13.

Ɗaya daga gidan ƴa-ƴan ƴan uwan marigayi Alhaji Bako, ya bayyana cewa marigayin ya bar wani gibin da babu wanda zai yi cike shi.

Ya kuma bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga iyalai da jihar Kaduna da kuma Najeriya baki ɗaya, inda ya ƙara da cewa marigayi Bako ya kasance shugaba abin koyi da aka sanya masa suna ‘Mai Gaskiya’ a lokacin da ya riƙe mukamin shugaban riƙo ƙwarya na ƙaramar hukumar Kaduna a shekarun alif 1980.