TIRƘASHI: Wani Uba ya sauyawa ƴarsa suna a jihar Katsina

Wani magidanci mai suna Yahuza Ibrahim Niga a ƙaramar Hukumar Jibia ta jihar Katsina ya chanzama ƴar sa suna a safiyar yau Asabar daga “Buhariyya” zuwa “Kausar”.

Majiyarmu ta Zuma Times Hausa ta ruwaito mahaifin ya sauyawa ƴarsa suna ne bisa rashin cika alƙawarin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC sukayi a yayin da suke neman ƙuri’un jama’a a shekarar 2015.

Malam Ibrahim ya ce shi ɗan gani-kashenin shugaba Buhari ne a baya, amma yanzu ya dawo rakiyar shi, yace tun a shekarar 2015 lokacin ana sauran kawana

Malam Ibrahim ya ce shi ɗan gani-kashenin shugaba Buhari ne a baya, amma yanzu ya dawo rakiyar shi, yace tun a shekarar 2015 lokacin da ana sauran kawana 26 Buhari ya kama aiki kuma aka yi sa’a matarshi tana gab da haihuwa yayi alƙawarin idan Allah ya sauƙeta lafiya idan ɗa ne zai saka sunan Buhari idan kuma mace ce zai saka mata suna Buhariyya. Yace yanzu ya warware wancan alƙawarin da ya cika ya canzawa ƴar suna.

Bugu da ƙari mahaifin yarinyar yace tun can ya jinkirta sanya yarinyar Makaranta ne saboda yanaso zai chanza mata suna kafin ta fara zuwa makaranta.