Sojoji sun hallaka ƴan bindiga a wasu luguden wuta a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sojoji sun hallaka fiye da ‘yan bindiga 50 a wani harin sama da ƙasa da suka kai a yankin Saulawa da Farin Ruwa da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar, ta ce nasarar ta biyo bayan hare-haren da jami’an tsaron haɗin gwiwa da jiragen sojin saman Najeriya suka kai a dazukan Dogon Dawa da Damari da Saulawa.

“Daga sama na’ura nuno ƴan fashi akan babura guda biyar, kusan kilomita 4 gabas da Saulawa, sun yi wa dakarun sojojin ƙasa kwanton bauna, inda jirgin saman yaƙi na farko ya buɗa musu wuta.

“Bayan wannan, an hangi wasu ƙarin ƴan bindiga ɗauke da babura kusan 50 suna arcewa zuwa ƙauyen Farin Ruwa, nan ma jirgin ya ƙara yi musu luguden wuta, sauran da suka tsira dakarun sojin ƙasan suka ƙarasa su”. A cewar sanarwar.

Bincike ya nuna cewa bayan hare-hare da jirgin yaƙin sojin saman Najeroya na biyu ya kai, an kashe ‘yan bindiga sama da 50 a yayin aikin haɗin gwiwar.

Samuel Aruwan ya ce Gwamna Nasir Ahmad El-Rufa’i ya nuna gamsuwar sa game da nasarar da Sojojin suka samu, ya kuma ya taya su murnar wannan nasarar. Ya buƙace su da su ci gaba da kawo karshen hare -haren da ‘yan bindiga ke kai wa.