Shugaba Buhari, Sarkin Musulmi, Sarkin Kano na daga cikin musulmai 500 masu faɗa a ji a duniya

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shi ne mutum na 16 cikin jerin sunayen musulmai 500 da ke da fada a ji a duniya.

Cikin jerin masu faɗa a duniyan, Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Teyyip Erdogan shine na farko, sai Sarkin Saudi Arabia Salman Bin-Abdulaziz Saud na biyu, yayin da shugaban ƙasar Iran Sayyid Ali Khameni ya zo na uku.

Sunayen wadda mujallar “Persons Of The Year” dake fitowa duk shekara ta wallafa, daga cikin waɗanda sunayen su ya fita a Najeriya baya shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’adu Abubakar na III a matsayin na 19, sai Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, Sheikh Ibrahim Saleh, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Yakubu Musa Katsina, Sheikh Ibrahim Zakzaky, Alhaji Aliko Dangote da dai sauran su.

A bangaren wasannin ƙwallon ƙafa a duniya akwai Mohammed Salah, Sadio Mane, Paul Pogba da Zinedine Zidane.