Saboda na nemi a tsige Kakakin Majalisa ne aka dakatar da ni- Ɗan Majalisar Zamfara

Ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar mazabar Anka, Yusuf Muhammad Anka ya bayyana cewa matakin dakatar da shi ba zai rasa nasaba da jagoranyar neman tsige kakakin majalisar saboda gazawar sa ba.

Anka wanda yayi magana da kafar Thunder Blowers ya ce, kasancewar sa jagoran tafiyar tsige kakakin majalisar wanda aka fara cikin watanni biyu da suka gabata, kakakin ya zabi ya fito da wannan sabon makirci.

Ya ce kafin yanzu ya fuskanci kakakin majalisar lokacin da ya samu labarin za a tsige shi, kakakin ya yi masa barazana idan ya ci gaba da shirin.

Dan majalisar ya kara da cewa hatta Gwamnan da kansa ya ƙira ya kuma yi masa barazana kan matakin tsige shi, lura da cewa, duk ƙoƙarin da aka yi na ganin Gwamnan ya fahimci yadda mafi munin halin da ‘yan majalisar dokokin jihar ke ciki ya gagara saboda ya ƙi ya saurare shi.

Ya ƙara da cewa bayan wasu kwanaki Gwamnan ya tura tsohon Ministan Kudi Bashir Yuguda don sasanta tsakanin su da kakakin majalisar da ɗaukacin mambobin da suka kafa ƙungiyar kuma suka amince suka dakatar da kudurin su saboda tsoma bakin tsohon Minista Yuguda.

Yusuf ya ci gaba da cewa gaba ɗayan ƴan majalisun sun roƙi Gwamnan da ya gyara abubuwa dangane da yadda yake gudanar da gwamnatinsa don cimma burin ciyar da jihar gaba.

Ya ce, abin mamaki, yayin da yake Kano yana halartar horon UNICEF, ya fara samun kira daga sassa daban -daban dangane da dakatarwar da aka yi masa bisa zargin alaƙa da ‘yan fashi da makami.

Ya ƙalubalanci mai gabatar da kudirin Yusuf Alhassan Kanoma da ya sanya lokacin da za su yi rantsuwa da Alkur’ani idan da gaske yake.

Yayin da yake nuna kyakkyawan fata cewa kwamitin da’a da alfarma zai yi masa adalci tare da abokan aikinsa, ya sake jaddada aniyarsa ta jan hankalin majalisar dokokin jihar zuwa kotu saboda bata masa suna da mutunci.

Ya bayyana zargin da abokin aikin sa Hon Kanoma ya yi cewa an ga shi da T. Tukur suna murna lokacin da suka ji labarin sace mahaifin kakakin ƙarya ne, domin ya ce lokacin da lamarin ya faru yana Kaduna yana halartar wani lacca amma ya kira ya jajantawa da kakakin kan abin da ya faru.

Ya kuma musanta zargin da Kanoma ya yi cewa shi da abokin aikin sa da ke wakiltar Bakura sun gudu daga wurin yin “rantsuwa” kan ‘yan fashi da makami da Gwamna ya gabatar kwanan nan.