Thursday, October 28, 2021
Gida Blog Shafi 99

YANZU YANZU: Majalisa ta umarci shuwagabannin tsaro su yi murabus

Duba da kara tabarbarewa da fannin tsaron kasar nan ke yi, yau Talata majalisar dattawa ta umarci shuwagabannin tsaro da su ajiye aikinsu su barwa waɗanda za su iya. Sanata Francis Fadahunsi daga jihar Osun ne ya taso da wannan batu kuma ya samu goyon baya daga sauran abokan aikinsa. Tuni...

YANKE SHAKKU: Alaƙar Cin Jan Nama da Ciwon Gwiwa

Miliyoyin mutane a faɗin duniya ne ke fama da ciwon gaɓɓai sakamakon larurori daban-daban. Matsalar ciwon gaɓɓai na da illar gaske ga ingancin rayuwa, tattalin arziƙi da walwala. A wani lokacin ma idan matsalar ta ta'azzara na iya nakasa mutum, sannan ta tsugunar da shi ɗungurugum. Sai dai wani abun...

An kwantar da mawakiya Maryam Sangandale a gadon asibiti

An kwantar da fitacciyar mawakiyar Hausa, Maryam A Baba da aka fi sani da ‘Sangandale’ a asibiti sakamakon matsananciyar rashin lafiya. Da yake fitar da labarin, abokin sana’arta, jarumi Abba El-Mustapha, ya bayyana cewar; Likitoci sun samu nasarar yi mata tiyata. Sai...

YANZU YANZU: Tsohon shugaban kasa ya sake kai wa Buhari ziyara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan. Majiyar HAUSA DAILY TIMES ta ruwaito Jonathan ya isa fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa da misalin karfe 11:00am sanna ya wuce kai tsaye zuwa Ofishin shugaban kasa domin fara tattaunawar.

Abin da ya sa dandaƙa bai dace da hukuncin fyaɗe ba~ Dr. Dukawa

Dakta Sa'idu Ahmad Dukawa, Malami a tsangayar kimiyyar Siayasa, a jami'ar Bayero (BUK) dake jihar Kano, ya bayyana cewa yi wa masu yin fyaɗe dandaƙa ba shine hukuncin da ya dace da su ba a jihar Kano. HAUSA DAILY TIMES ta ruwaito Dr. Ahmad Dukawa ya bayyana haka ne a...

YANZU YANZU: Shugaban hukumar NDDC ya suma a gaban kwamitin bincike

Shugaban hukunar raya yankin Neja Dalta wato NDDC, Mista Daniel Pondei ya suma a gaban kwamitin majalisar tarayya dake bincike kan yadda hukumar ta kashe wasu kudade da suka kai biliyan dari uku na naira da majalisar ta gano. Pondei ya suma ne a lokacin da ake tambayarsa kan...

GAGARABADAU: Wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da wannan dattijo

Wannan dattijo da kuke gani dai ɗan wata kabila ce da ake kira da Mumuye a jihar Taraba. Kabila mafi yawan al'umma da kuma yankuna a jihar.Shi dai wannan bawan Allah da kuke gani za ku yi mamaki idan kuka ji shekarunsa. An haifeshi a Alif 1949. Wanda a yau shekarunsa 71 kenan...

Masu shiga tsakani a Mali sun yi kira a kafa gwamnatin haɗin gwuiwa

Masu shiga tsakani daga yankin Afirka ta Yamma da ke ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin siyasar ƙasar sun bayar da shawarar kafa gwamnatin haɗin gwuiwa da kuma sabuwar kotun tsarin mulki bayan da dubban masu zanga-zanga suka fita titunan ƙasar suna nuna fushinsu.

Za a gurfanar da wani Sanata a kotu bisa karya doka

Wani sanata a ƙasar Kenya ya nemi afuwa bisa karya dokar hana fita ta yamma zuwa asuba da aka saka domin daƙile yaɗuwar cutar korona. Sanata Johnson Sakaja mai wakiltar birnin Nairobi, an gan shi a ƙarshen mako yana shan...

Ba za a gurfanar da mutumin da ya yi wa mata 40 fyaɗe ba a gaban kotu

Mutumin nan da rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta kama a watan da ya gabata kan zargin yi wa mata fiye da 40 fyade ba zai gurfana a gaban kotu ba a yau kamar yadda aka tsara.