Thursday, October 28, 2021
Gida Blog Shafi 3

Najeriya za ta yi babban baƙo daga ƙasar Turkiyya

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Teyyip Edogan zai kawo ziyarar aiki Najeriya a ranar Laraba. Cikin wata sanarwa da Kakakin fadar shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ya fitar, Erdogan zai kawo ziyarar ne tare da maiɗakinsa Emine Erdogan inda za su shafe kwanaki biyu. Shugaban yana ziyarar aiki a ƙasashen nahiyar Africa...

Sojoji sun hallaka ƴan bindiga a wasu luguden wuta a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sojoji sun hallaka fiye da 'yan bindiga 50 a wani harin sama da ƙasa da suka kai a yankin Saulawa da Farin Ruwa da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari. Cikin wata sanarwa da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar, ta ce nasarar ta...

Ƴan sanda sun cafke wani da ake zargi da kisan kai saboda wata karuwa

Jami'an 'yan sandan jihar Ogun sun kama wani mutum mai suna Bisi Omoniyi dan shekara 25 da laifin kashe wani dattijo dan shekara 50 kan wata mata da ake zargin yana son kwana da ita. DSP Abimbola Oyeyemi, jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan jihar, ya tabbatar da faruwar...

Ƴan bindiga sun kashe mutum 49 a wani hari a jihar Sokoto

Rahotanni daga jihar Sokoto sun ce ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutum 49 a wata kasuwa a garin Goronyo na jihar. Wasu ganau sun tabbatar wa da BBC labarin inda suka ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da yamma, yayin da mutanen ke cin babbar kasuwar Goronyon. Mutanen waɗanda...

Kwankwaso ya magantu game da labarin kwanarsa a hannun EFCC

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi magana game da labarin da wasu manyan Jaridun Najeriya suka wallafa kan cewa hukumar EFCC dake yaƙi da cin hanci da rashawa ta kama shi har ma ya kwana a hannunta. Tsohon Gwamnan jihar Kanon wanda hotunan sa suka bayyana a safiyar Lahadi a...

Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Bungudu ya kubuta daga hannun ƴan bindiga

Masarautar Bungudu da ke jihar Zamfara ta tabbatar da labarin kubutar Sarkin Fulanin Bungudu Alhaji Hassan Attahiru wanda aka sace a hanyar Kaduna zuwa Abuja kwabaki 32 da suka wuce. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Masarautar ta fitar Hausa Daily Times ta samu a daren Asabar.

Ƙananan ƴan kasuwa 600 sun amfana da tallafin miliyan sha-biyar a Gusau da Tsafe

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Gusau da Tsafe Hon. Kabiru Ahmadu (Mai Palace) ya ƙaddamar da raba tallafin kuɗi naira miliyan N15,000,000 ga ƙananan ƴan kasuwa a mazabarsa. An ƙaddamar da raba tallafin ne ga ƙananan ƴan kasuwa da manoman rani. Rukunin...

NITDA ta horar da mata Ƴan Jarida kan Fasahar Sadarwar Zamani

Daga Isma'il Karatu Abdullahi Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa NITDA ta horar da mata ‘yan jarida 50 da aka zabo daga jihohin Arewa maso Yamma kan aikin jarida na zamani kuma ta raba musu kwamfutoci 50 da nufin zamanar musu da aikin su. Taron bitar na kwana biyu da...

Ana zargin ƴar aiki da sace sarƙoƙin gwal da darajar su ta kai miliyan goma a Kaduna

‘Yan sanda a ranar Juma’a a Kaduna sun gurfanar da wata ƴar aiki mai suna Aisha Abdullahi ‘yar shekara 23, wacce ake zargin ta sace ƴan kunne da sarƙokin gwal na matar da take yi wa da darajarsu ta kai kimanin Naira miliyan 10. Aisha, ta bayyana a gaban wata...

Ɗan shekara 71 ya mutu yayin da yake zina da karuwa a Ogun

Ajibola Olufemi Adeniyi, dattijo mai shekaru 71, da aka ruwaito a ranar Litinin, ya mutu a lokacin da yake tsaka da yin zina a wani Otal da ake ƙira 50/50 da ke Ogijo, a karamar hukumar Sagamu ta jihar Ogun. An tattaro cewa mamacin, mazaunin gida mai lamba 22, titin...