Thursday, October 28, 2021
Gida Blog Shafi 2

Akwai babban darasi a rayuwata- Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa) ya bayyana cewa akwai darasi a rayuwarsa duba da yadda ya taso tun yana ƙarami. Wazirin Adamawa yana magana ne a hanyoyin magance matsalar ilimi a wurin bikin yaye ɗalibai na jami'ar 'Baze University' a Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar...

Shugaba Buhari, Sarkin Musulmi, Sarkin Kano na daga cikin musulmai 500 masu faɗa a ji a duniya

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shi ne mutum na 16 cikin jerin sunayen musulmai 500 da ke da fada a ji a duniya. Cikin jerin masu faɗa a duniyan, Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Teyyip Erdogan shine na farko, sai Sarkin Saudi Arabia Salman Bin-Abdulaziz Saud na biyu, yayin da shugaban ƙasar...

Gwamna Matawalle ya buɗe wani babban asibiti da ya gina a Zamfara

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Juma’a, ya ƙaddamar da buɗe babban asibitin mai gadaje 300 a karamar hukumar Birnin-Magaji ta jihar. Dakta Bashir Maru, Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Asibitocin jihar shi ne ya wakilci gwamnan a yayin ƙaddamar da asibitin.

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji sun hallaka sabon shugaban mayaƙan ISWAP, Malam Baƙo

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Mongonu (mai ritaya) ya sanar da mutuwar Malam Bako, wanda ya maye gurbin Abu Musab Al-Barnawi, shugaban ƙungiyar mayaƙan ISWAP. Mongonu ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa kan sakamakon ganawar shugabannin hafsoshin tsaro,...

Ƴan bindiga sun dasa bama-bamai a hanyar jirgin ƙasa Abuja-Kaduna

Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa, NRC, a ranar Alhamis ta tabbatar da fashewar wani abin fashewa ga ɗaya daga cikin jiragenta da ke jigila a hanyar Kaduna zuwa Abuja, wanda wasu da ba a san ko su waye ba suka dasa akan haryar jirgin. Manajan darakta na NRC, Fidet...

Wa ya ɗirkawa ƙannen sa uku mata ciki

An samu wani matashi ɗan shekaru 24 da ya yi wa ƙannensa mata su uku ciki a jihar Legas. Mahaifiyar su, ta bayyana cewa, mahaifin yaran ba mazauni bane sannan ita ma ta buɗe shago da take gudanar da harkokin kasuwancinta. Matar ta bayyana cewar, suna barin...

An sake yin garkuwa da sama da fasinjoji 30 a jiha Neja

Rahotanni sun ce sama da fasinjoji talatin ne ƴan bindiga suka sake yin garkuwa da su a ƙauyen Garun Gabas da ke ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja. Ƴan bindigan sun sace fasinjojin ne da ke cikin wata mota ƙirar Bas da wasu ƙanana biyu.

Darasi daga rayuwar marigayi Alhaji Aliyu Mai-Bornu.

Daga; Adamu Kazaure (Ɗan Almajiri) Marigayi Alh. Aliyu Mai-Bornu an haifeshi a shekarar 1919 a birnin Yola da ke Jihar Adamawa. Ya samu nasarar shiga Jami'ar Bristol dake ƙasar Ingila domin karantar Economics a lokacin yana da shekaru 35, ya kuma kammala karatun sa a Jami'ar Bristol yana da shekaru 38 a duniya,...

Ƙaunar da nake yi wa Annabi Muhammadu ce ta sa na rera waƙar yabonsa- Jaruma Sarah Aloysius

Fitacciyar jarumar fina -finai a cikin shirin DadinKowa na gidan talabijin na Arewa24, Sarah Aloysius, ta ce matuƙar girmamawar da take yi wa Annabin Musulunci, Muhammad (S. A. W) ne ta sa aka ganta tana rera wakokin yabonsa cikin harshen Larabci a wani faifan bidiyo a shafukanta na Sada Zumunta.

An kama wasu masu kai wa ƴan bindiga man-fetur daga Kano zuwa Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da samar da man fetur ga ƴan bindiga a jihar Katsina, daga Kano, jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Talata, a Kano. Ya bayyana sunayen...