Saturday, November 27, 2021
Gida Blog Shafi 108

Gwamna Bagudu ya naɗa kwamitin raba taki da kayan noman damunan bana

Daga Abdulrahman Ramadan Dabai Gwamnatin jihar Kebbi a ranar Talata, ta kaddamar da wani kwamiti da zai kula da rarrabawa da kuma sayar da takin zamani da sauran kayan aikin gona domin noman damunan bana. Shugaban Ma’aikatan fadar Gwamnatin johar, Alhaji Suleiman Mohammad Argungu ne ya jagoranci...

Gwamnatin Zamfara ta baiwa ƙungiyar IZALAH gudunmawar naira miliyan 100

Daga Ibrahim Baba Suleiman Gwamnan Zamfara Bello Matawallen Maradun, ya baiwa kungiyar JIBWIS gudunmawar Naira miliyan Dari (₦100,000,000.00) domin fara gudanar da jami'ar musulunci da kungiyar take shirin gudanarwa a garin shinkafin jihar Zamfara. Gwamna Matawalle yace "wannan jami'a da kungiyar JIBWIS...

Tsoffin ɗaliban kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Sokoko sun kai ziyarar jaje ga shugabancin makarantar

Tsoffin daliban tsangayar koyon aikin jarida (Mass Communication) na kwalejin kimiyya da fasaha da suka kammala a shekarar 2016, sun kai ziyarar jaje domin nuna bakin cikin su dangane da iftila'in gobara da ta afkawa tsangayar a kwanakin baya, wanda hakan ya yi sanadiyyar konewar Ofisoshin wasu malamai da dakunan koyar da watsa...

Majalisar koli ta JIBWIS ta ziyarci Bafarawa domin godiya ga kyautar makaranta

Daga Ibrahim Baba Suleiman Majlisar koli ta kungiyar JIBWIS, tare da wasu wakilan kwamitoci a matakin kasa da wasu takaitattun shugabannin jihohi sun ziyarci Tsohon gwamnan jihar Sokoto Dakta Attahiru Dalhatu Bafarawa, domin yi masa godiya akan kyautar makekiyar makaranta wanda ya kashe mata sama da miliyan dubu daya da...

Ban taba cin haram ba, ban taba karban haram ba, kuma bana cin haram~ Sheikh Pantami

Ministan Sadarwa da kuma tattalun arziki na zamani Sheikh Dr Isah Ali Ibrahim Pantami yace bai taba cin haram ba, bai taba karban haram ba, kuma ba zai taba cin haram da sanin sa. Wani dalibin Malamin mai suna Datti Assalafiy ne...

Rundunar ƴan sanda za ta deba sabbin jami’ai

Rundinar 'yan sandan Nigeria karkashin jagorancin Maigirma shugaban rundinar 'yan sanda IGP Muhammad Abubakar Adamu tana sanar da al'umma cewa zata debi sabbin jami'ai masu mukamin Constable. Idan Allah Ya kaimu nan da kwana uku wato ranar talata 14-7-2020 za'a bude shafin yanar gizo wanda za'a shiga a cike ga...

Shugaba Buhari ya amince da fitar da N108bn don ginin titi a jihohi hudu

Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC, karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba ta amince da fitar da Naira Biliyan 108 don gini da gyaran tituna guda hudu. Za a gudanar da ayyukan titin ne a jihohin Adamawa, Borno, Enugu da Rivers kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Ku maida hankali iyakokin jiha domin inganta tsaro~ Mataimakin Gwamnan Kebbi ga ƴan sa kai

Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Sama'ila Yombe Dabai ya yi kira ga kungiyar 'Yan Sakai ('yan banga) da su mayar da hankali iyakokin jihar da sauran jihohi domin dakile kwararowar 'yan ta'adda jihar. Mai girma mataimakin gwamnan ya yi wannan kira ne a yayin da yake zantawa da manema labarai...

Duk matashi ya ji daɗin abin da ya faru tsakanin Festus Keyamo da ‘yan majalisa, kalubale ga Ministan Matasa~ Hon. Sadiq

Wani jajirtaccen mataahi kuma ɗan siyasa da ya taba neman tsayawa takarar kujerar dan majalisar wakilai daga babban birnin tarayya Abuja, Hon. TPL Abubakar Sadiq Ahmad Kwali ya ce abin da karamin Ministan Kwadago Festus Keyamo ya yi abin jijinawa ne ga duk wani matashi a Najeriya idan har ya tabbata gaskiya abin...