Najeriya za ta yi babban baƙo daga ƙasar Turkiyya

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Teyyip Edogan zai kawo ziyarar aiki Najeriya a ranar Laraba.

Cikin wata sanarwa da Kakakin fadar shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ya fitar, Erdogan zai kawo ziyarar ne tare da maiɗakinsa Emine Erdogan inda za su shafe kwanaki biyu.

Shugaban yana ziyarar aiki a ƙasashen nahiyar Africa domin ƙarfafa dangantakar ƙasar da ƙasashen.