“Maƙiyana basa farin ciki da shigana fina-finan India”- Rahama Sadau

Fitacciyar Jarumar fina-finai Rahama Sadau, wadda a yanzu haka take taka muhimmiyar rawa cikin wani shirin fim a ƙasar Indiya, mai suna ‘ Khuda Haafiz’, ta nuna godiya ga Allah bisa bata damar da ta daɗe tana nema na samun shiga cikin fina -finan masu shahara, fitattun wakoki da tallace-tallace ciki da wajen Najeriya.

A cikin wani sabon saƙo da ta wallafa a shafukanta na kafafen sada zumunta, jarumar da ke da zama a Kaduna ta ce duk da cewa an dakatar da ita ko kuma an kore ta daga Kannywood, duk lokacin da ta shiga wata matsala, Allah yana sa hakan ya zame mata alƙhairi.

Wannan ne ya sa ta kafa wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Today’s Care’ don kula da mabukata tare da gode wa Allah da ya ɗaga likafarta, ya kuma kare ta daga abokan gaba da waɗanda ba sa mata fatan alheri ko son ganin ci gaban ta a harkar wasan kwaikwayo.

Sadau ta ƙara da cewa tuni ta zama shahararriyar tauraruwa ta ƙasa da ƙasa, kuma ƴar kasuwa da ke cikin rufin asiri, don haka wannan ba yana nufin ba za ta koma Kannywood ta ci gaba da wasan kwaikwayo ba.

“Zan koma cikin babban shiri kuma in zama babban furodusa, a zahiri, ina tunanin buɗe gidan Cinema a Kaduna don mutane su riƙa zuwa hutawa tare da iyayen su a lokacin bukukuwa,” in ji ta.

“A duk lokacin da na yanke shawara na shiga wasu ayyuka, abin da nake tunani shine mahaliccina, ba masu zagi cikin ayyukana ba, iyayena suna raye, gami da ‘yan uwana, koyaushe suna yi min addu’a, don Allah ya kiyaye ni daga abokan gaba kuma gaskiya, addu’arsu ta zama katanga mai ƙarfi tsakanina da makiyana.

“A koyaushe ina samun nasara a aikin da na zaɓa na yin wasan kwaikwayo, a yau, ina Indiya muna daukar wani sabon fim a matsayin babbar jaruma da ke jagorar fim ɗin, ina jin yaren Indiya sosai wanda ƙari wata dama ce a gare ni, a lokacin da nake birnin New York da wasu fitattun mawaƙa, na riga da na shiga Nollywood, yanzu sunan Rahama Sadau ya shiga kundin ‘Hall of Fame’ inda manyan mutane maza da mata ne kawai za su iya shiga kundin”, in ji ta .