Ku canza halayen ku don gyaruwar Najeriya ~Inji Mataimakin Gwamnan Kebbi.

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Dakta Sama’ila Yombe Dabai ya yi ƙira ga al’umma da su canza halayyan su domin gyaruwar ƙasa baki ɗaya.

Mai Girma, Dr Sama’ila Yombe Dabai mni ya bayyana hakan a yayin rufe tafsirin Ramadan na wannan shekarar a Masallacin Dr. Bello da ke Birnin Kebbi a ranar Asabar kamar yadda hakan ya zo a takardar sanarwa da mai magana da yawunsa, Atom Turba Ishaku ya fitar.

Mataimakin Gwamnan ya kuma ya lura don shawo kan matsalolin Najeriya, dole ne mutane su miƙa lamuransu ga Allah, suyi abin da ya dace kuma su nemi gafarar sa.

Tafsirin Ramadan na bana wanda Sheikh Usman Muhammad Sani, Babban Limamin Masallacin Dr Bello ya gudanar, ya karkatar da Tafsirin na bana akan kadaita Allah da gaskatawa.

Ya kara da jan hankalin ‘yan Najeriya da su ƙara himma wurin addu’a domin samun zaman lafiya, hadin kai, fahimtar juna tare da yin addu’ar Allah ya saka wa wadanda suka ba da gudummawa wajen samun nasarar kammaluwar Tafsirin Ramadan na bana.

A wajen taron, an yaba wa mataimakin gwamnan kan irin gudummawar da yake bayarwa da kuma nuna goyon baya ga ayyukan addinin Islama a ciki da wajen jihar sannan an yi masa addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya kara masa lafiya da buɗi cikin lamuransa.

An gudanar da addu’oi na musamman ga yanayin tsaro a jihar da ma Najeriya baki daya.