Jiragen yaƙi sun yi luguden wuta a dazukan Sokoto da Katsina

Dakarun sojojin rundunar Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da tarwatsa maboyar su a Dajin Sokoto da Katsina, a cewar rahoton PRNigeria.

A jihar Sakkwato, a yayin hare-hare da rundunar sojin saman Najeriya ta kai, ta farmaki dazukan Mashema, Yanfako, Gebe, da Gatawa da ke cikin ƙananan hukumomin Isah da Sabon Birni na jihar.

Wata majiyar soji ta shaida wa PRNigeria cewa an cimma wannan nasarar ne ta hanyar kai hare -hare ta sama da aka kai a ranar 5 ga Oktoba 2021, bayan jerin ayyukan sa -ido ta sama, inda aka gano wuraren.

“Mun gano inda ƴan bindiga daga sansanin Turji da Maigona da mayakansu ke haɗuwa don tsarawa tare da ƙaddamar da hare-hare.

“Dangane da haka ne, rundunar sojin sama ta shirya jiragen yaƙi masu sauƙar ungulu don afkawa wuraren. A cewar majiyoyi a yankin, jiragen saman sun kai hari a yankunan da aka nufa, inda suka tarwatsa wasu gine -gine tare da kashe wasu da yawa daga ‘yan bindigar.

Wasu mazauna garin sun hango waɗanda suka tsira daga hannun ‘yan ta’addan suna tserewa a wata makarantar firamare da ke ƙauyen Bafarawa.”

A jihar Katsina, PRNigeria ta tattaro cewa maboyar ‘yan ta’adda a yankunan dajin Rugu mai iyaka da Karamar Hukumar Kankara, jiragen rundinar Sojin sama sun yi luguden wuta tsakanin 30 ga Satumba zuwa 3 ga Oktoba 2021.

An tarwatsa sansanin ɗan ta’adda nan Gajere tare da kashe ƴan bindiga 34 a harin.

Haka kuma, kimanin mutane 20 da ake zargi suna daga cikin ƴan ta’addan sun samu munanan raunuka daban -daban.