JIBWIS ta umarci Limamai da Malamai su sanya ƙasa cikin adu’a

Daga Ahmad Muhammad Bindawa

Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga al’umma, da a kara fadada ayyukan komitin marayu, ta inda zai kara da karba da kuma tattara zakkatul fitr da kuma rabata akan lokaci ga mabukata domin suma suyi sallah cikin farin ciki da walwala.

Shugaban ya bada umurnin a fara wannan aiki nan take a dukkan unguwannin dake fadin kasar nan, Yayin magana akan As-salam University, Shugaban yace kudirin da akayi na tara biliyan daya domin gina University, tun bayan rantsar da ginin jami’an da akayi, wanda akace kowa zai bada taimakon naira dubu daya har yanzu ba’a kai ba, saboda haka shugaban yayi kira da muyi amfani da wannan wata mai albarka mu cigaba da saka wannan taimako na naira dubu daya domin yanzu haka aikin gina jami’a yayi nisa a garin Hadejia.

Sannan shugaban ya kara jan hankalin mutane musamman masu kudi dasu taimakawa ginin wannan jami’a wajen bada wani kaso na zakkan da suke bayarwa, shugaban yace koda bayan kammala ginin jami’ar, lallai in akan samu zakah to lallai zai taimaka wajen gudanar da ayyukan Jami’ar domin kamar yadda kowa ya sani gudanar da jami’a ba karamin abu bane.

Sannan Shugaban yayi kira ga dukkan wanda sukayi alkawari yayin rantsar da fara ginin jami’an da suyi kokari su cika, sannan ya roki Allah ya basu kwarin gwuiwa wajen cika wannan alkawari. Sannan Shugaban ya nuna farin cika da godiya ga dukkan yan’uwa da sukayi alkawari kuma suka cika sannan yayi adduar Allah ya saka musu da alkhairi, ya biyasu da gidan aljannah.

Sannan dukkan wani mai zummar bada nashi gudun muwa wajen gina As-salam University zai iya tura wannan taimako ta wannan asusu;

Acc Name:As-salam Int’l University
Acc No: 0006027065
Bank: Ja’iz

A karshe Shugaban na Izala ta tarayyar Nigeria, Sheikh Abdullahi Bala lau, yayi umurni ga al’ummar musulmi dasu dage wajen addu’oi da kuma neman yafiyar ubangiji, domin hakan kawai shine zai kawo mana mafita ga wannan kangi na rashin tsaro da muka samu kanmu a ciki a wannan kasa.

Sannan shugaban ya kara da cewa, kula da maraya hakkine ga dukkan musulmi, saboda haka, kada taimakonmu ga marayu ya tsaya ga basu abinci da kaya kawai a watan ramadan. Yanada matukar muhimmanci ga al’ummar musulmi, su dage wajen bawa marayu ilimi ta hanyar daukan nauyin karatunsu. Shugaban ya kara da cewa lallai a cikin masu kudinmu, akwai wadanda zasu iya daukan nauyin karatun marayu dari, inda yace in ma mutum bazai iya ba, to mutum ya dauki koda nauyin karatun maraya guda daya ne.

Jibwis Nigeria