Inganta tsaro shine babban abin da muka sa a gaba – Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya ce inganta tsaro, tattalin arziƙi da yaƙi da cin hanci da rashawa har yanzu su ne muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.

Shugaban ya yi wannan tsokaci ne a Kaduna yayin da yake jawabi a bikin yaye Sojoji karo na 68 a kwalejin NDA.

“Kamar yadda kuka sani, ƙasar mu Najeriya tana fuskantar kalubalen tsaro da yawa a wannan lokacin. Muna ci gaba da fuskantar barazanar tsaro da miyagun aiyyuka irin su tawaye, fashi da makami, garkuwa da mutane da kashe -kashen siyasa wanda ke barazana ga haɗin kan ƙasa, ”in ji shi, a cewar wata sanarwa da kakakinsa, Garba Shehu ya sanya wa hannu.

“Ina tabbatar muku da cewa wannan gwamnatin za ta ci gaba da yin duk abin da doka ta tanadar don kawar da duk wasu manyan laifuka da ke haifar da tsoro da fargaba a tsakanin ƴan ƙasa.

“Yana da kyau a faɗa game da wannan cewa, mun samu sabbin kayan aiki a yaƙin da muke yi da duk wani nau’in rashin tsaro daga ƙasashen da muke abokantaka.

“Za a yi amfani da wadannan kayan aiki don inganta yaƙi da rashin tsaro a dukkan sassan ƙasar.”

Shugaba Buhari ya lura cewa tsaro ya zama babban abin maida hankali akai a cikin shugabanci da manufofin jama’a a cikin tsarin duniya.

“Dangane da wannan yanayin ne muka gabatar da wani sabon jirgin ruwa a farkon wannan shekarar don maye gurbin tsoffin jiragen ruwa na sojojin ruwan Najeriya,” in ji shi.

“Ana sa ran gabatar da Jirgin Ruwa zai kara karfin Sojojin Ruwa da inganta kasuwancin mu na teku, zaman lafiya da aminci a yankin Tekun Guinea da makwabtan mu ta ruwa.”

Shugaban ya ce gwamnatin ta shirya tsaf don kawar da abubuwan da ke haifar da cin hanci da rashawa ta hanyar magance wasu dalilai masu nisa a matsayin wani bangare na dabarun na dogon lokaci don yaƙi mafi inganci da ɗorewa kan aikin.

Ya ce an ci gaba da inganta rayuwar ‘yan ƙasa tare da haɗin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu.