Gwamnonin jihohi za su goyi bayan cire tallafin man fetur baki ɗaya – El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce gwamnatocin jihohi a shirye suke su marawa gwamnatin tarayya baya wajen ganin an kawar da tsarin tallafin man fetur.

El-Rufa’i ya ba da wannan tabbacin ne a ranar Talata a Abuja, a wajen taron Bankin Duniya na ci gaban Najeriya, mai taken “Lokacin Kasuwancin da ba a saba da shi ba”.

Malam El-Rufa’i, ɗaya daga cikin mahalarta taron, ya ce idan ba a kawar da tsarin tallafin man fetur ba, to jihohi 35 daga cikin 36 na tarayya ba za su iya biyan albashi ba a shekarar 2022.

A cewarsa, an kayyade kananzir wadda ta fi damun talakawa ba tare da wata matsala ba, yayin da kuma man dizal wanda ke da matukar muhimmanci ga masu safara an dade ana kayyade shi.

El-Rufai ya ce gwamnonin sun ga hatsarin da ke tattare da ci gaba da bin hanyar tallafin man fetur da kuma matakan tallafawa manufofin da ake bukata don inganta yanayin kasafin kudi, kamar daidaiton farashi.

Wannan, in ji shi, ta hanyar tabbatar da cewa an daidaita farashin musaya da kuma kyakkyawan aiki tsakanin manufofin kasafin kudi da na kudi.