Gwamnatin Zamfara ta baiwa ƙungiyar IZALAH gudunmawar naira miliyan 100

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Gwamnan Zamfara Bello Matawallen Maradun, ya baiwa kungiyar JIBWIS gudunmawar Naira miliyan Dari (₦100,000,000.00) domin fara gudanar da jami’ar musulunci da kungiyar take shirin gudanarwa a garin shinkafin jihar Zamfara.

Gwamna Matawalle yace “wannan jami’a da kungiyar JIBWIS take shirin farawa a jihar mu namu ne gaba daya, kuma zamuyi iya yinmu domin ganin harkar ilimi ya farfado, musamman a jihar Zamfara” .

Gwamnan a cewarsa, wannan gudunmawa da ya bada, somin tabi ne, zai kuma kara badawa nan gaba domin ganin jami’ar ta tsaya akan kafafuwan ta.

Tun farko a bayanansa, Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, yace mun shigo jihar Zamfara ne domin nunawa majalisar koli ta JIBWIS makarantar, wanda tsohon gwamnan Jihar Sokoto ya bamu, tare da kokarin kammala ta a cikin watanni shida, daga nan kuma muka wuce Gusau domin mu shaidawa gwamnan cewa zamu yi jami’a a jihar sa, wanda hakan ya bashi sha’awa har ya bada wannan gudunmawar nan take.