Gwamnatin Kaduna ta yi umarni da a buɗe hanyoyin sadarwa

Gwamnatin jihar Kaduna ta ɗage dokar hana amfani da hanyoyin sadarwa na watanni uku data saka a wasu kananan hukumomi tun a watan Oktoba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne saboda yawaitar hare-haren ƴan bindiga a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu’a.

Aruwan ya bayyana cewa tuni gwamnati ta baiwa hukumomin dake da alhaki kan lamarin su maida hanyoyin sadarwa a yankunan da abin ya shafa.