Gwamnatin Jihar Neja ta hana sayar da babura

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya haramta sayar da babura a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Ahmed Matane ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Minna, inda ya ce dokar ta biyo bayan kalubalen tsaro da ake fama da shi a wasu sassan jihar.

Ya ce an kuma sanar da haramcin ne saboda yanzu ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane suna neman babura a matsayin kudin fansa.

Ya bayyana cewa haramcin ya shafi siyar da babur (Bajaj, Boxer, Qiujeng, Honda ACE, Jingchen) mai karfin injin daga 185 Cubic Centimeter (cc) zuwa sama”.

Mista Matane ya kuma bayyana cewa matakin na da nufin kawar da ayyukan ƴan ta’adda, ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane wadanda ke tayar da ƙayar baya ga waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.

Ya yi Allah-wadai da irin kisan gilla da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane su ke yi a sassan jihar tare da jaddada aniyarsu na kawar da matsalar tsaro a jihar.

Mista Matane ya ƙara da cewa gwamnati na sane da matsalolin da matakin zai janyo wa jama’a, amma an ɗauki matakin ne domin amfanin jihar baki ɗaya.

Ya kuma yi ƙira ga dillalan babura a jihar da su bi wannan umarni.

Ya bukaci ‘yan jihar da su bai wa Jami’an tsaro hadin kai kan matakan tsaro da ake dauka domin kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda.

Sakataren gwamnatin jihar ya kuma bayyana cewa gwamnati ta umarci jami’an tsaro a jihar da su tabbatar da bin doka da oda.

Mista Matane ya kara tabbatar da cewa har yanzu dokar haramta yin Okada da tashoshin mota ba bisa ka’ida ba a Minna da kewaye na nan.