Gwamnatin Buhari za ta rabawa ƴan Najeriya tallafin mai

Gwamnatin Tarayya za ta raba wa dukkan ƴan Najeriya N5,000 na rage raɗaɗin tallafin mai da ta janye daga shekarar 2022.

Gwamnatin ta ce za ta raba wa tallafin sufuri ne a madadin tallafin mai da za ta janye gaba ɗaya.

BBC Hausa ta rawaito cewa Ministar kuɗi Zainab Ahmed Shamsuna ce ta bayyana haka a ranar Talata a wani taron Bankin Duniya kan ci gaban Najeriya.

Ministar ta ce adadin waɗanda za su amfana da tallafin ya dogara ne da yawan abin da ke hannu bayan janye tallafin.

“Kafin kammala janye tallafin mai a tsakiyar 2022, muna aiki tare da abokan hulɗarmu kan matakai da suka kamata na rage tasirin janye tallafin ga talakawa.”

“Ɗaya daga cikin matakan shi ne tsarin biyan tallafin sufuri ta hanyar tura wa ƴan Najeriya tsakanin miliyan 30 zuwa 40 kuɗi,” in ji ta.

Alƙalumman Bankin Duniya sun nuna cewa kashi 40 na talakawan Najeriya, kashi uku kawai na fetur suke amfani da shi a ƙasar, tare da nuna cewa masu arziki ne suke amfana da tallafin mai da gwamnati ke biya.