Ganduje zai hukunta Abduljabbar daidai da yadda doka ta tanadar

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta bibiyi batun Sheikh Abduljabbar Kabara “har zuwa ƙarshensa.”

BBC ta ruwaito Mai magana da yawun Ganduje, Abba Anwar, ya ambato shi yana bayyana hakan ranar Juma’a yayin wata ziyara da ya kai wa Sheikh Ƙariballah Kabara, wanda yaya ne ga malamin.

Yana magana ne mako guda bayan an kai malamin gidan yari sakamakon gurfanar da shi a gaban wata kotun shari’ar Musulinci da ke jihar.

An gurfanar da malamin a gaban kotun ne a ranar Juma’a, bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.

Gwamna Ganduje ya ƙara da cewa “muna matuƙar farin ciki ganin cewa muna bin matakan da suka dace game da wannan batu. Kuma gwamnatin jiha za ta ci gaba da bibiyar lamarin sosai har zuwa ƙarshensa.”

Gwamnan na Kano ya yaba wa malaman jihar ta Kano da suka tafka muƙabala da Sheikh Abduljabbar game da zarginsa da yin batanci ga manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), yana mai cewa “fafutukar tamu ce duka.”.