Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaban Majalisar Sarakunan jihar Taraba, Aku Uka, ya mutu

Sarkin Masarautar Kwararrafa dake Wukari kuma shugaban majalisar Sarakunan jihar Taraba, Shekarau Angyu Masa-Ibi (Aku Uka) ya mutu.

Rahotanni daga jihar Taraba sun ce Sarkin Jukun na 27 ya rasu bayan fama da jinyya.

Ya shafe shekaru 45 bisa ƙaragar Sarautar. Ya hau ƙaragar mulkin Kwararrafa a shakarar alif 1976.

Shi ne Uban Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutse, jihar Jigawa.