Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Kano ya ƙetare rijiya da baya

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero, ya tsallake wani yunƙuri na kai masa hari da wani da ba a san ko waye ba ya yi ƙoƙarin afkawa motarsa.

Sahelian Times ta ruwaito wani ganau ya shaida mata cewa lamarin ya faru ne lokacin da Sarkin ke komawa fadarsa a kusa da titin Zariya, a cikin birnin Kano.

Tuni dai ‘yan sanda suka kama wanda ake zargin. Sai dai, ba a bayyana dalilin kai harin ba kuma ƴan sanda ma ba su ba da sanarwar abin da suka gano ba.