Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Bungudu ya kubuta daga hannun ƴan bindiga

Masarautar Bungudu da ke jihar Zamfara ta tabbatar da labarin kubutar Sarkin Fulanin Bungudu Alhaji Hassan Attahiru wanda aka sace a hanyar Kaduna zuwa Abuja kwabaki 32 da suka wuce.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Masarautar ta fitar Hausa Daily Times ta samu a daren Asabar.

Sanarwar ta ce, “Sarkin Bungudu (Sarkin Fulanin Bungudu) Alhaji Hassan Attahiru ya samu kubuta daga hannun masu garkuwa bayan shafe kwana 32 ahannun su.

Amadadin iyalan Sarki da masarautar Bungudu muna mika sakon godiya zuwa ga al’umma domin addu’a da taimako ta hanyoyi daban daban da suka bayar tun faruwar wannan al’amari har zuwa you.

Muna miqa godiya zuwa ga gwamnatin jihar Kaduna bisa kokarin da sukayi tayi tun ranar da akayi garkuwa da Sarki har zuwa lokacin daya samu dawowa.

Muna miqa godiya ta musamman zuwa ga gwamnatin jihar Zamfara karkashin shugabancin Hon. Dr. Bello Mohammed (Matawallen Maradun) bisa gagarumin kokarin da tayi domin ganin Sarki yasamu dawowa gida lafiya.

Muna jinjina zuwa ga hukumar yan’ sanda da kungiyar Miyetti Allah bisa kokarin da sukayi na ganin Sarki yadawo gida lafiya.

Muna roqon al’umma dasu cigaba da yima Sarki addu’a zuwa wasu yan kwanaki nan gaba da zai nemi lafiya da kuma samun natsuwa kafin yadawo ya gana da al’umma”. A cewar Takardar Sanarwar.

An yi garkuwa da Mai Martaba Sarkin Bungudu a ranar 15 ga watan Satumba a hanyar sa ta zuwa Abuja daga Kaduna, inda aka samu hasaran rai na ɗan sanda ɗaya dake tare da Sarkin.