Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Tarayya ta ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ayyana kungiyoyin ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda.

A wani hukunci da mai shari’a Taiwo Taiwo ya zartar a ranar Juma’a, kotun ta ce ayyukan ƙungiyoyin ‘yan Bindiga da ‘Yan Ta’adda, sun zama ayyukan ta’addanci.

Hukuncin ya biyo bayan buƙatar da gwamnatin tarayya ta shigar ta hannun ma’aikatar shari’a ta tarayya.

A cikin wata takardar rantsuwar da Gwamnatin Tarayya ta shigar na goyon bayan buƙatar, ta shaida wa kotun cewa, rahotannin sirri sun tabbatar da cewa ƙungiyoyin ‘yan bindigar sun kitsa kashe-kashe da sace-sace da fyaɗe da sace-sacen mutane da sauran ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso gabas, arewa ta tsakiya da sauran sassan ƙasar.

Daraktan hukumar shigar da ƙara ta ƙasa, Abubakar, ya shaida wa kotun cewa, sakamakon abin da ‘yan ta’addan suka aikata, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya amince da sanya su a matsayin ƙungiyar ta’addanci.

Mai shari’a Taiwo, ya amince da wannan ƙudiri kamar yadda ya nema, inda ya bayyana ayyukan ƙungiyar Ƴan Bindiga da na Ƴan Ta’adda da sauran ƙungiyoyi makamantansu a kowane bangare na ƙasar nan, musamman a yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya a matsayin ayyukan da suke yi ta’addanci ne.

Kotun ta kuma haramta ayyukan ƙungiyoyin da sauran ƙungiyoyi makamantansu a kowane yanki na Najeriya.

Mai shari’a Taiwo ya kuma umurci Gwmnatin Tarayya da ta ayyana ƙungiyoyin a matsayin ƴan ta’adda ta hanyar sanarwa tare da bugawa a manyan jaridu biyu na ƙasa.