Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Tarayya ta sanar da yaushe Nigeria Air zai fara aiki

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, ya ce ana sa ran kamfabin sufurin jirgen saman Najeria Air zai fara nan da watan Afrilun 2022.

Ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.

A cewarsa, Sufurin zai kasance wani kamfani wanda gwamnatin Najeriya za ta rike hannun jarin kashi 5%, ‘yan kasuwan Najeriya na da kashi 46%, yayin da sauran kashi 49% za a kebe su ne domin har yanzu ba a basu abokan huldar kasuwanci ba, ciki har da masu zuba jari daga ƙasashen waje.

Ya ce idan ya fara aiki, kamfanin sufurin jiragen na ƙasa zai samar da ayyukan yi kusan 70,000 ga ‘yan Najeriya.