Buhari ya gana da Sheikh Ɗahiru Bauchi a Abuja

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, a fadar gwamnati ta Aso Rock Villa a jiya Laraba.

Ganawar bata rasa nasaba da kisan gilla da aka yi wa musulmai da suka halarci zikirin sabuwar shekara a gidan Sheikh Dahiru Bauchi a hanyar su ta komawa jihohin su a daidai ƙauyen Rukuba dake Jos ta Arewa.

A hira da ƴan jaridu a Abuja, Shehin Malamin, ya ce sun bar komai a hannun gwamnati amma in ta kasa ɗaukar mataki su za su san abun yi.