Bincike: Yadda aka kashe Captain Abdulkareem Bala Na’Allah a Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce an yi wa Kyaftin Abdulkarim, ɗan Sanata Bala Ibn Na’Allah, kisan gilla ne ta hanyar shaƙe masa wuya da igiya.

Hausa Daily Times ta ruwaito a ranar Asabar bata-gari sun kashe matashin a gidansa dake unguwar Malali a Kaduna.

Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar ta bayyana cewa hukumomin tsaro sun sanar da gwamnatin jihar cewa an samu gawar wani Kyaftin Abdulkarim, ɗan Sanata Na’Allah a gidansa da ke Kaduna.

“A wani abu mai kama da kisan gilla, an tsinci mamacin a cikin ɗakin kwana na gidansa da ke Malali, Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, a ɗaure da igiya. Maharan sun sace wata mota daga wurin da yake ajiye motoci,” inji Aruwan.

Ya ce a yankin Janwuriya na Ƙaranar Hukumar  Kajuru, wasu ’yan bindiga sun kashe wani Ahmadu Tanko.

Aruwan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna matuƙar bacin ransa kan rahotannin sannan ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka mutu sannan ya aike da ta’aziyya ga iyalansu.

“Gwamna ya bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi don cafke waɗanda suka kai harin kuma a halin yanzu jami’an tsaro suna bincike kan abubuwan da suka faru,” a cewarsa.