BINCIKE: Amfanin cin Namijin Goro ga lafiyar Ɗan’Adam

Binciken masana a cibiyar binciken magunguna ta ƙasa da ke Yaba, Lagos dangane da amfanin da cin namijin goro ke yi a jiki ya nuna cewa:

1. Yana magance matsalar ido.

2. Yana ƙara lafiyar huhu, ƙoda da hanta.

3. Yana maganin tari, mura, massara, gudawa, yawan atishawa, tarin fuka.

A wani bangaren an ƙara bayyana cewa:

4. Yana ƙara taushin murya ta hanyar washe maƙogoro.

4. Yana karya guba a cikin jiki.

5. Yana karya kwayan cututtuka da ke cikin abincin da aka ci.

6. Yana maganin zazzabi.

Binciken wanda Dr Bartholomew Brai da Dr Emeka Amaechi daga cibiyar ta binciken magunguna ya bayyana musu cewa babu wani illa da cin namijin goro ke kawo wa ga jiki.

Madogarar mu ta kamfanin dillancin labari ya ce masana sun bayyana cin namijin goro zai iya hana magani da wani majinyaci ke sha aiki sosai a jiki wato yana rage masa kaifin aiki da ya ke yi a jiki.