Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Alhaji Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa, ya taya al’ummar musulmin Najeriya murnar shiga sabon watan Maulidi, wata da ake bikin murnar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W).
Ya bayyana haka ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Saƙon ya ce, “Ina mika sakon taya murna ga dukkan al’ummar Musulmin Najeriya yayin da muke marhabin da wannan wata na Maulidi.
“Hakika lokacin Maulidi, lokaci ne da masana Sira, wato tarihin Manzon Allah (SAW) ke karantar damu asalin tarihi da gwagwarmaya, karamci, Tausayi da Rahama irin na Manzon tsira Annabi Muhammad (SAW).
- Lauya ya roƙi attajiran Najeriya su kawo ƙarshen yajin aikin ASUU
- An sake kama wani fursuna da ya tsere daga gidan yarin Jos
“Wata ne da ake ilimantar da mutane game da Al’Qur’ani mai girma da kara cusa soyayyar Manzon Allah SAW a zukatan mu.
“Hakika wannan lokaci ne da mu ke kokarin koyon wadannan halaye na Manzon tsira domin nuna Tausayi da yafiya a tsakanin mu.
“Ina kira ga al’ummar Musulmin Najeriya, suyi amfani da wannan lokacin wajen tsananta addu’ar neman zaman lafiya da Hadin kai da ci gaba mai dorewa a wannan kasa tamu.
Barkan mu da shiga wannan wata na Rab’ul Auwal”.