An gano abubuwan da ke yawan haddasa hatsari a kogin Yauri

Matasa a Yauri na jihar Kebbi sun koka bisa yadda ake ci gaba da samun ƙaruwan hatsarin jirgin ruwa a yankin.

Matasan sun yi wannan ƙira ne bisa iftila’in hatsarin ruwa da ya faru a kwana-kwanan nan da ya laƙume rayuka sama da mutum dari da har yanzu ba a ga wasu gawakin ba ciki har da (mata, maza, da yara).

Jirgin wanda aka ƙiyasta ya ɗauki mutum sama da 160, ya yi hatsari ne bayan ya tashi zuwa garin Warra dake ƙaramar hukumar Ngaski a jihar Kebbi.

Al’ummar masarautar Yauri sun koki bisa rashin bin ƙa’idan lodin kaya da ɗaukar jama’a da masu jiragen ruwa ke yi ga kuma rashin sanya rigunan kariya.

Wasu mazauna Yauri da Hausa Daily Times ta yi hira da su sun shaida mata cewa akwai wasu manyan itatuwa da ke tsaye a tsakiyan kogin wanda sukan bacewa a duk lokacin da ruwa ya zo sossai.

Wani matashi Jabir Abubakar Yauri a wani dogon rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ja hankalin hukumomi da alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma ya rata a wuyar su da su yi abin da ya dace wurin magance yawan aukuwar hatsarin ruwa da ake samu a yankin Yauri.

Daga cikin rubutun da Jabir Yauri ya wallafa ya baiwa hukumomi shawara kamar haka.

1. Da farko ya nemi da ta Sare manyan itatuwa da suke tsakiyar kogin Yauri,

2. Yawaita kwashe duwatsu da laka da ruwan ke jawowa,

3. Ƙara yawan rigunan kariyan ruwa tare da haramta tafiya kan ruwa babu rigunar kariya,

4. Tilasta bin dokar hana yawan ɗaukar mutane bisa ƙima da

5. Yashe kogin tare da ƙara masa zurfi da kwashe duk wasu abubuwa masu hatsari.