Abin da ya faru da Maryam Booth na shirn faruwa da mawaƙiya Tiwa Savage

Fitacciyar mawakiyar Ingausar Turanci da Yarabanci Tiwa Savage ta ce ana yi mata barazanar kwarmata wani hoton bidiyonta da saurayinta na baɗala.

A lokacin da take tattaunawa da wata tashar rediyo a ƙasar Amurka, mawakiyar ta ce ba za ta biya ko sisi ga mutumin da ya ke mata barazana ba.

Da fari an soma tura sakon barazanar ne ga manajanta a ranar Laraba wanda kuma nan take ya sanar da ita da kuma adadin kudin da aka nema ko a wallafa bidiyon, kamar yadda BBC ta wallafa.

Ta kuma shaida cewa saurayinta ne a bisa kuskure ya soma ɗaura hoton a shafin sada zumunta kuma nan take ya goge, sai dai tuni mai yi mata barazanar ya yi sa’ar sauke bidiyon.

Tiwa ta ce a halin yanzu saurayinta na cikin damuwa.

Mawakiyar ta ce da farko ba ta ji dadin faruwar lamarin ba, amma dai kuma ba za ta amince a yi amfani da wannan damar wajen ɓata mata suna ko durkusar da ita ba.