Friday, December 4, 2020
Gida Blog Shafi 2

Ku daina baiwa masu garkuwa kuɗin fansa, ku riƙa bari suna kashe waɗanda suke kamawa~ Wani Malami

Mataimakin Limamin Masallacin Juma’a na Triumph da ke Jihar Kano, Dakta Abdulmudallib Ahmed, ya ce hanya daya tilo da za a dakatar da satar mutane don neman kuɗin fansa a Arewa ita ta barin masu garkuwan su kashe wanda suka kama. Babban Shehin malamin wanda ya bayar da wannan shawarar...

Da Ɗumi Ɗumi: Majalisar dattawa ta aikewa Ministan Sadarwa Pantami sammaci

Majalisar dattawa (Senate) ta gayyaci Ministan Sadarwa Sheikh Isah Ali Ibrahim Pantami da ya bayyana a gabata domin yi mata bayani kan yadda tasaro ya ƙara tabarbarewa a Najeriya. Ana sa ran ƴan majaliar za su nemi Ministan ya musu bayani akan yadda masu garkuwa da mutane ke ci gaba...

DA ƊUMI-ƊUMI: Buhari zai buɗe Bodojin Najeriya

Gwamnatin Buhari ta bayyana yiwuwar sake buɗe kan iyakokin ƙasa wato Boda da aka rufe tun watan Agusta 2019 ba da daɗewa ba. Ministar Kuɗi da Tsare-Tsaren ƙasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ce ta bayar da wannan tabbaci a lokacin da take zantawa da manema labarai na Fadar shugaban ƙasa a...

Sabuwar kasuwar Madallah alheri ce ga jihar Neja- Sakataren Gwamnati

Daga Ismat Suleja Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Ibrahim Matane ya yaba wa Kamfanin Dodo Consult da ke aikin gina sabuwar Kasuwar Madallah da ke Karamar Hukumar Suleja a Jihar Neja. Alhaji Ibrahim Matane baya bayyana haka ne a lokacin ziyarar gani da ido da su Ka...

DA ƊUMI-ƊUMI: An sace shugaban jam’iyar APC na jihar Nassarawa

Ƴan bindiga sun yi awun gaba da shugaban jam'iyar APC reshen jihar Nassarawa Hon. Phillip Tetari Shekwo. Kwamishinan ƴan sandan jihar Bola Longe, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce an sace shugaban ne a gidansa dake Lafiya babban birnin jihar da misalin ƙarfe 11pm na daren jiya Asabar.

DA ƊUMI-ƊUMI: ASUU ta janye yajin aiki

Ƙungiyar Malaman jami'o'i ta ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe watanni takwas tanayi bayan cimma matsaya da gwamnatin tarayya.

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin tarayya ta yi wa ASUU tayin N65bn domin ta janye yajin aiki

Gwamnatin tarayya ta yiwa ƙungiyar ASUU tayin naira biliyan N65bn a matsayin kuɗin alawus alawus ɗinsu tare da na gyaran makarantun su domin neman su janye yajin aiki da suke yi na tsawon watanni takwas. Ministan ƙwadago Criss Ngige ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala zaman ci gaba...

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnan Kebbi ya naɗa sabon shugaban ma’aikatan jihar

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya nada Alhaji Safiyanu Garba Bena a matsayin shugaban ma'aikatan jihar na riƙon ƙwarya. Sabon naɗin ya biyo bayan ƙarewan wa'adin aikin tsohuwar shugabar ma'aikatan jihar Hajiya Fatima Sani Ango wadda ta yi ritaya tun a makon jiya. Kafin naɗin sabon shugaban ma'aikatan jihar, Alhaji...

DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan Boko Haram sun harbo jirgin Helikoptan gwamnati a Borno

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun harbo wani jirgin sama mai sauƙar ungulu na ƙasar Nijar ɗauke da wasu fasinjoji da ba a tantance ko su waye ba a karamar hukumar Bama da ke jihar Borno. Majiyar Hausa Daily Times ta jaridar Daily Trust ta turanci...

TALLAFIN ƘANANAN ƳAN KASUWA: An yabawa mataimakin Gwamnan jihar Kebbi

An jinjina ma mai girma mataimakin gwamnan jihar Kebbi Kanal Sama'ila Yombe Dabai mai ritaya (TAMBARIN ZURU) akan samun tallafi wanda hukumar samarda ayuka ta ƙasa wato NDE ƙarkashin Dr Nasir Ladan Argungu ta bayar a karamar hukumar mulki ta Zuru a satin da ya gabata. A wani jawabi da...

Biyo mu

0FansLike
0FollowersFollow
217FollowersFollow
0SubscribersSubscribe