Gwamna Zulum ya raba wa iyalan manoma da aka kashe N600,0000 tare da kayan abinci ga

Gwamnan jihar Borno ta hannu kwamitin da ya kafa ya raba tallafin kuɗi naira dubu dari shida (N600,000) ga iyalan manoma 43 da Boko Haram ta kashe a Zabarmari.

Farfesa Babagana Zulum ya bayyana cewa kuaɗeɗen tallafi ne da ƙungiyar gwamnoni ta bayar na naira miliyan N20m da kuma wanda hukumar bunƙasa Arewa ta Gabae NEDC ta bayar, naira Miliyan N5m.

Baya ga kayan abinci, kwamitin gwamnan ya raba buhunan kayan abinci dubu 13,0000 tare da dubban jarakunan mai, taliya da sauransu.