Dalilin da ya sa na raɗawa tagwayen da aka haifa min sunan Buhari da Al-Makura~ Gwamnan Nassarawa

Gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Sule ya raɗawa tagwaye da matarasa ta biyu ta haifa masa sunan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da Sanata Umar Tanko Almakura, tsohon gwamnan jihar.

Hausa Daily Times raɗawa tagwayen sunan shugaban ƙasa da tsohon gwamnan jihar ya janyo cecekuce a cikin al’umma.

Sai dai gwamnan ya ce yayi haka ne bisa gairma da daraja da waɗan nan shuwagabannin biyu wato shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da Sanata Umar Tanko Almakura suke da shi a rayuwarsa.