DA ƊUMI-ƊUMI: Muhimman hanyoyin jihar Kebbi biyu sun samu sahalewar gwamnatin tarayya za a fara aikin su

Majalisar zartarwa ta amince da sakin Naira Biliyan N117bn domin fara gayaran wasu sabbin tituna a faɗin Najeriya.

Hakan ya biyo bayan zaman majalisar na yau da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ministan Aiyuka da gida Babatunde Fashola ya sanar da ƴan jaridun fadar shugaban ƙasa yadda aikin zai kasance da kuma inda za a gudanar da su.

Ya ce a matakin farko shugaba Buhari ya amince da ware naira biliyan N18.9Bn domin gyara tituna da gina sabbin gadoji.

Ya ƙara da cewa sauran kuɗin kuma an amince da a fitar da su domin gyara hanyoyi a sauran jihohi ciki har da ta Koko zuwa Dabai a jihar Kebbi da lalacewarta ya yi muni matuƙa, akan N19.713 billion. Da kuma hanyar Jegga-Kwana-Sanagi-Gumi a jihar akan N31.539 billion.