ZABARMARI: Zai fi dacewa a nemo tsofaffin Sojoji maimakon ɗauko na haya daga ƙasashen waje domin yaƙar Boko Haram~ Kanal Yombe Dabai

Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Kanal Sama’ila Yombe Dabai (mai ritaya) ya shawarci gwamnatin tarayya da ta tuna da tsofaffin Sojoji a yayin da take neman yadda za ta kawo ƙarshen yaƙi da ƴan Boko Haram a Arewa maso Gabas biyo bayan kisan gillar da aka yiwa manoma a jihar Borno.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake maida martani ga shawarwari 6 da gwamnan jihar Borno ya baiwa shugaban kasa da jaridar Daily Trust ta wallafa, inda yake neman a kawo sojojin haya na kasashen waje don yakar ƴan Boko Haram, kamar yadda mataimaki na musamman ga mataimakin gwamnan Atom Turba Ishaku ya fitar a wata takarda.

Samaila Yombe Dabai ya ce “Kamar yadda na ke tausaya wa ‘yan Najeriya kan matsalar rashin tsaro, zan ba da shawara mai karfi cewa zai fi dacewa a dawo da tsofaffin ƙwararrun sojoji dake raye kuma da ƙarfi domin yaƙi da ƴan ta’addan nan maimakon daukar sojojin haya”

Ya bayyana yadda Janar Gowon ya tuna da tsoffin Sojoji da suka yi yakin duniya na biyu don tallafa wa sojojin da ke bakin daga a lokacin yaƙin Biafra.

Ya ce amfani da tsofaffin dakarun tsaro zai rage yawan kuɗi da kayan aiki da gwamnati za ta samar domin su tsofaffin Sojoji ne da suke da kwarewa a fagen yaƙi da sarrafa makamai fiye da na haya da za a ɗauka.

Samaila Yombe Dabai daga karshe ya sake nanata shawara ga gwamnati da ta nemi gudunawar tsofaffin sojoji maimakon ɗaukan na haya da za su taya dakarun ƙasa yaƙi da ƴan Boko Haram.