DA ƊUMI-ƊUMI: An kashe mutum bakwai a wani harin ramukon gayya a Kaduna

Rahotanni da muke samu daga jihar Kaduna sun ce an kashe aƙalla mutane bakwai wasu sabbin hare-haren ɗaukar fansa da aka kai ƙaramar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Lahadi a ƙauyen Ungwan Bido inda aka kashe wasu mazauna yankin sannan aka raunata wasu huɗu. Har ila yau, yara biyu da ba a san inda suke ba.

Kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce harin na yau Lahadi ya biyo bayan rahoton da aka bayar na kashe wani makiyayi, Isiyaka Saidu a ƙauyen Ungwan Pah a ranar Asabar da wasu mutane da ba a san su ba suka yi.

Gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa’i ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da suka yi sanadin asarar rayuka a karamar hukumar Jema’a, ya kuma umarci hukumomin tsaro da su binciko tare da cafke duk wadanda ke da hannu a aikata laifin.

Yayin da yake jajantawa iyalan mamata da wadanɗan da suka jikkata, El-Rufa’i ya yi ƙira ga hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, da shugabannin al’umma da su ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar don dorewar kokarin samar da zaman lafiyar al’umma wanda gwamnatin jihar Kaduna ke tallafawa.

Ya kuma umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ta hanzarta samar da kayayyakin agaji ga ‘yan kasar da gidajensu suka kone da kuma wadanda suka jikkata a harin.