DA ƊUMI-ƊUMI: An samu sauƙar ruwa a jihar Neja

Rahotanni da suke shigo mana daga ƙaramar hukumar Paikoro dake jihar Neja sun bayyana an samu sauƙar ruwan sama a garin Paiko a lokacin da al’umma suka gama cire tsammanin sake samun sauƙar ruwa.

Hausa Daily Times ta tuntubi wasu mazauna garin Paiko mutum biyu kuma suka tabbatar mata da lamarin wanda suka bayyana a matsayin ‘abin mamaki’.

Tun a farkon watan Oktoba ruwa ya tsaya cak a jihar, sabanin yanda aka saba a jihar a duk damuna inda a wani lokaci damuna takan kai har watan Disamba a wasu yankuna jihar.

Da yake wasu sukan yi girbin amfanin gonan damuna sau biyu, a wannan shekara an samu hasaran amfanin gona domin duk wanda ya saba shuka sau biyu kokuma wanda ya yi shuka a makare shukar ta ƙone bisa rashin ruwan sama in mai buƙatar yawan ruwa ce.