DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin tarayya ta yi wa ASUU tayin N65bn domin ta janye yajin aiki

Gwamnatin tarayya ta yiwa ƙungiyar ASUU tayin naira biliyan N65bn a matsayin kuɗin alawus alawus ɗinsu tare da na gyaran makarantun su domin neman su janye yajin aiki da suke yi na tsawon watanni takwas.

Ministan ƙwadago Criss Ngige ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala zaman ci gaba da tattaunawa tsakanin ma’aikatarsa da ƙugiyar ta ASUU.

Ya ce hakan ya zo a matsayin ƙari ne ga tayin biliyan hamsin da gwamnatin ta yiwa ƙungiyar domin su janye yajin aiki da suke yi.

Har yanzu dai ƙungiyar ASUU ta malaman jami’o’i bata ce komai ba.