Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnan Kebbi ya naɗa sabon shugaban ma’aikatan jihar

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya nada Alhaji Safiyanu Garba Bena a matsayin shugaban ma’aikatan jihar na riƙon ƙwarya.

Sabon naɗin ya biyo bayan ƙarewan wa’adin aikin tsohuwar shugabar ma’aikatan jihar Hajiya Fatima Sani Ango wadda ta yi ritaya tun a makon jiya.

Kafin naɗin sabon shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Safiyanu Garba Bena shine babban sakataren sashin aiyyuka na musamman na jihar.