DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan Boko Haram sun harbo jirgin Helikoptan gwamnati a Borno

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun harbo wani jirgin sama mai sauƙar ungulu na ƙasar Nijar ɗauke da wasu fasinjoji da ba a tantance ko su waye ba a karamar hukumar Bama da ke jihar Borno.

Majiyar Hausa Daily Times ta jaridar Daily Trust ta turanci ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kusa da garin Banki da misalin karfe 10 na safiyar yau Talata, mutum biyar dake cikin jirgin sun mutu a hatsarin nan take.

Wata majiya da ta kai agajin gaggawa tare da Sojoji ta tabbatar jirgin na ƙasar Nijar ne kuma alamu sun nuna kabo jirgin aka yi.

Izuwa lakocin haɗa wannan rahoto rundinar Soji bata ce komai ba akan afkuwar lamarin.