TALLAFIN ƘANANAN ƳAN KASUWA: An yabawa mataimakin Gwamnan jihar Kebbi

An jinjina ma mai girma mataimakin gwamnan jihar Kebbi Kanal Sama’ila Yombe Dabai mai ritaya (TAMBARIN ZURU) akan samun tallafi wanda hukumar samarda ayuka ta ƙasa wato NDE ƙarkashin Dr Nasir Ladan Argungu ta bayar a karamar hukumar mulki ta Zuru a satin da ya gabata.

A wani jawabi da Ofishin mai taimakawa mataimakin gwamnan kan harkokin sadarwa na zamani Atom Turba Ishaku ya fitar, ya ce jinjinan ya fito ne daga bakin wasu da suka ci gajiyan wannan tallafi ta dalilin mataimakin gwamnan.

Jawabin ya ci gaba da cewa taron raba tallafin dai an gudanar ne a babban ɗakin taron Zuru na ‘Komo Unity Hall’ inda akalla mutane ɗari biyar suka anfana da tallafin dubu goma goma.

A jawabin Mallam Yahaya a madadin wa’enda suka ci gajiyan tallafin ta hannun mataimakin gwamna, yace ” Babu abinda zamuce sai dai Allah saka mishi da Alkhairi, kuma muna yima Yombe Dabai fatan kariya daga sharri.

“Mun anfana da wannan tallafi kuma insha Allahu wasu suma zasu karu damu dallilin wannan ta hanyar sana’oin mu”.

Yahaya, yw kuma buƙaci da a isar musu da sakon godiya zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari, Gwamna Atiku Bagudu dashi kanshi Samaila Yombe Dabai da fatan wannan taimakon za’a cigaba dashi don gina al’umma.