DA DUMI-ƊUMI: Wani Gwamnan ya sauya sheƙa

Jam’iyar APC ta ƙasa ta sanar da reshenta na jihar Ebonyi cewa gwamnan jihar David Umahi ya sauya sheƙa daga jam’iyar PDP zuwa APC.

Sauya sheƙar gwamnan na zuwa ne ƙasa da awanni 24 da ya gana da shugabancin jam’iyar PDP a Abuja wanda majiya mai tushe ta shaidawa majiyar Hausa Daily Times ta jaridar Daily Trust cewa jam’iyar tayi kokarin hana gwamnan barinta a zaman na jiya.

Duk da cewar gwamnan bai bayyana barin jam’iyar da bakinsa ba, amma ana sa ran zai koma jihar yau ko gobe Alhamis domin tabbatar wa al’ummar jihar ya sauya sheƙa.