2.3 C
London
Tuesday, February 18, 2025

Gwamnan Neja ya haramta wa manyan motoci hawa saman gadar Dikko

Daga Latifa Shuaibu Gani

Gwamnan jihar Neja Umar Muhammad Bago ya umarci jami’an tsaro da hukumar kare haɗuran kan hanya (FRSC) da su tabbatar daga yanzu babu wata motar da ta bi ta saman kan gadar Dikko da ba a kammala ba domin bin hannu ɗaya na babban titin Kaduna-Abuja.

Gwamnan ya yi wannan umarni ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido inda tankar man fetur ta ƙone jiya Asabar a kusa da ”Dikko Junction” da ke ƙarƙashin karamar hukumar Gurara ta jihar, inda sama da mutum 77 su ka ƙone ƙurmus yayin da wasu 55 ke kwance a gadon asibiti.

Gwamnan Neja da tawagarsa a wurin da tankar mai ya ƙone a Dikko Junction.

Cikin wani jawabin manema labarai da Sakataran Yaɗa Labaransa Ibrahim Bologi ya fitar, Gwamnan wanda ya koka kan yadda sakacin wasu direbobin mota ke salwantar da rayukan bayin Allah, ya ce ba zai lamunci motoci su ci gaba da bin saman gadar ta Dikko ba, sai dai su bi ta ainahin hanyar da ake bi ta ƙarƙashin gadar komai rintsi.

Ya yi ƙira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa wajen ƙarasa aikin hanyar Minna zuwa Suleja, domin rashin kammala aikin ne ke jawo hasarar rayukan al’umma.

Sabbin Labarai
Labarai Masu Alaka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here