2.3 C
London
Tuesday, February 18, 2025

Dokar Haraji: Matakin da gwamnoni su ka ɗauka bai wadatar ba- Sanata Ndume

Daga Latifa Shuaibu Gani

Sanata Muhammad Ali Ndume da ke wakiltar jihar Borno ta Kudu a Majalisar Dattijai ya bayyana goyon bayansa ga shawarwarin da kungiyar gwamnonin Najeriya ta bayar kan sabuwar dokar haraji, sai dai ya ce har yanzu akwai wasu sashin dokar da zai yi kyau a ƙara yi wa jama’a bayani akai.

Ndume wanda shi ya fara sukar dokar a lokacin da aka gabatar da ita a majalisar dattijai, ya ce dokar za ta ƙara tagayyara talakawa maimakon ta kawo musu sauƙi matsin da su ke ciki.

Yayin wata hira da BBC Hausa, Sanatan ya ce matakin da gwamnoni su ka ɗauka abin a yaba ne, to sai dai akwai buƙatar a buɗe ƙofar faɗaɗa tuntuɓa tare da jin ra’ayin jama’a kafin a ɗauki matakin tabbatar da dokar a hukumance.

Sabbin Labarai
Labarai Masu Alaka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here